Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake Yayi Shigar 'Yan Sanda Ya Kashe Mutane A Mogadishu


Wani Harin Ta'addanci

Akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu, sannan wasu 15 suka jikkata bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a babban ginin horar da ‘yan sandan kasar da ke babban birnin Mogadishu a yau Alhamis.

Akalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu, sannan wasu 15 suka jikkata bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a babban ginin horar da ‘yan sandan kasar da ke babban birnin Mogadishu a yau Alhamis.

Wannan hari ya faru ne yayin da ‘yan sanda suke bitar fareti a cibiyar horar da ‘yan sanda ta Janar Kahiye Police Academy. Jami’ai sun ce maharin yayi shigar burtu ne, inda ya saka kaya irin na ‘yan sanda. Sai dai hukumomi ba su ba da takamaiman adadin wadanda suka mutu ba, kuma tuni Kungiyar Al Shebab suka dauki alhakin kai wannan harin.

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da aka hada bayan binciken da aka gudanar cikin watanni 20 da suka gabata, ya nuna cewa baya ga jami'an tsaro, hare-haren kungiyar Al Shebab na ci gaba da shafar fararen hula.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG