Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Matar Dan Wasan Fina-finan Ghana a Amurka


‘Yan sanda a wata unguwar nan Washington suna farautar wanda ya kashe Bettie Jennifer, uwargidan wani shahararren dan wasan fina finai a Ghana Chris Attoh.

‘Yan sanda sun ce an harbe Jenifer har lahira ne a ranar Juma’a a Greenbelt dake jihar Maryland yayin da ta bar ginin ofishin da take aiki a ciki.

Wani da ya shedi lamarin yace Jenifer ta ga wani mutum da bindiga a hannunsa a filin ajiyar mota. Tayi kokarin kauce masa kana ta fara gudu, amma duk da haka sai da dan bindigar ya zuba harsashai sau biyu.

‘Yan sanda sun ce suna zaton itace maharin ya auna ya kashe kana ya kuma arce daga wurin.

Mai gidanta Attoh yana aiki a birnin Los Angeles a kan wani fim, nan da nan ya katse aiki ya dau jirgi zuwa Maryland

Rahotanni sun ce masu bincike sun fara nazari a kan sakwannin da Attoh ke kafewa a shafinsa na sada zumunta bayan ya fidda hotunan shi da ita a shafukan yanar gizo.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG