Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane 35 A Idlib, Inji Kungiyar Syrian Observatory


Dakaru a Syria
Dakaru a Syria

Wata kungiya mai sa ido a kan yakin Syria, ta ce an kai farmaki ta sama a kan wata unguwa mai tarin gidaje dake karkashin rikon kungiyar ‘yan tawayen kasar kuma an kashe akalla mutane 35 kana aka jikata wasu da dama, ciki har da kananan yara.

Kungiyar da take zama a Birtaniya mai sa ido a kan take hakkin bil adama a Syria ta Syrian Observatory, ta ce farmakin ya auna kauyen Zardana dake arewa maso yammacin gundumar Idlib.

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP a wurin, ya ce tarin mutanen da suka ji rauni da ake kulawa dasu a asibitocin yankin, sun hada ne da mata da kananan yara da tsofaffi da kuma ma’aikatan ceto.

Sai dai an kawana biyu ba’a sami irin wannan farmaki ta sama a kan garin na Idlib ba a cikin yan watannin da suka gabata.

Dubun dubatar mutane da suka rasa matsugunansu daga wurare a cikin kasar ta Syria, yanzu suna zaune ne a Idlib.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG