Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Da Kim Jong Un Zasu Gana A Tsibirin Santosa Dake Singapore


Donald Trump da Kim Jong Un
Donald Trump da Kim Jong Un

Yanzu ta tabbata cewa Shugaba Trump da shugaba Kim Jong Un zasu yi taron kolinsu a masaukin baki dake Capella na Tsibirin Santosa dake cikin kasar Singapore makon gobe

Fadar Shugaban Amurka ta White House ta ce ganawar Shugaba Donald Trump da Shugaban Koriya Ta Arewa Kim Jong Un a makon gobe, za a yi ta ne a otal din Capella na Tsibirin Sentosa da ke kasar Singaore.

Sakatariyar Yada Labaran Fadar White House Sarah Huckabee ta bayyana wurin da za a yi ganawar da ake matukar dokin ganin an yi din ne ta kafar twitter jiya Talata. Ta kara da cewa, "Mun gode ma masu masaukin baki, mutanen Singapore, saboda wannan karamcin."

Tun da farko, Trump ya bayyana fatan cewa tattaunawar da za a yi ran 12 ga watan Yuni a Singapore za ta kasance "Mafarin wani abu babba ... kwanan nan za mu gani!"

Jami'an gwamnatin Amurka da na Koriya Ta Arewa na cigaba da yin sharar fage gabanin ganawar.

Makon jiya Trump ya gana a Fadar White House da wani babban hadimin Kim Jong Un, mai suna Kim Yong Chol, wanda ya mika masa wasika daga Shugaban Koriya Ta Arewa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG