Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutane 68


Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kai hari akan wani kauye a arewa maso gabashin Najeriya, sannan suka kashe a kalla mutane 68.

Shaidu sun gaya wa Muryar Amurka cewa mayakan sun kai hari akan garin Njaba dake Jihar Borno kafin wayewar garin Talata.

Wata mazauniyar Njaba, Aminnatur Mommodu mai shekaru misalin 40 tace an kyale mata sun tafi, amma duk wani namiji har da yara masu shekaru 12, 13 da 14 sun gamu da ajalin su a wajen ‘yan bindigan. Ta ce mata sun arce zuwa daji a lokacin da mayakan suka kai hari, sannan da suka dawo sun kirga gawarwaki 68, kowanne a cikinsu an harbe shi da bindiga, ko kuma an yi mishi yankan rago.

Saboda nisan wajen daga manyan garuruwa, an samu kwanaki biyu kafin duniya ta ji labarin abun da ya faru, musamman a babban birnin jihar wato Maiduguri, dake da tazarar misalin kilomita 100 daga kauyen.

Wannan hari na shige da ire-iren hare-haren da mayakan Boko Haram ke kai wa a wasu kauyuka da garuruwa a arewa maso gabashin Najeriya.

Tashe-tashen hankula na farfadowa biyo bayan farmakin da dakarun Najeriya, Nijar da Chadi, da Kamaru suke kaiwa domin kwato ikon yankunan da mayakan sa kai suka mamaye a shekaru biyu da suka gabata.

Alhamis dinnan Rundunar Sojin Najeriya tace ta kwato ikon garin Mafa dake Jihar Borno.

XS
SM
MD
LG