Accessibility links

An Kashe Mutane da Kona Gidaje a Kwandiga


Wani bangaren ofishin ‘yan sanda da 'yan bindiga suka aka kaiwa hari a Najeriya.

Misalin karfe biyar na yamma ran Talata agogon Najeriya, wasu ‘yan bindiga sanye da kayan sarki, kuma sun kaiwa mutane farmaki, da kuma bude wuta akan gidajensu a garin Kwandiga dake jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, kuma sun kashe a kalla mutane 39 da raunata wasu, kuma sun kona gidaje da yawa.

Ana kyautata zaton ‘ya’yan kungiyar nan ne da aka fi sani da Boko Haram, sune suka kai wannan hari, duk da cewa babu wanda ya fito ya dauki alhakin harin.

Wakilin Muryar Amurka Haruna Dauda Biu ya garzaya inda wannan abu ya faru, inda aka zube gawarwaki na mata da maza da yara a kasa. Wasu daga cikin wadanda suka mutu yanka su akayi, wasu kuma aka harbe su da bindiga, wasu kuma aka kona su da wuta.

An jere gawarwakin ne a babban Masallacin garin, su wajen 39, sannan suka kona kaso 75 cikin dari na gidajen garin baki daya.

‘Yan bindigan suna kasuwanni, da asibitoci da kuma ma’aikatu.

A halin yanzu dai, tarzomar ta lafa, inda aka kai jami’an tsaro wannan gari domin tabbatar da zaman lafiya, sannan gwamnati tayi alkawarin cewa zata kai tallafin kayan agaji ga mutanen da wannan lamari ya shafa.

A halin yanzu dai, mata da yara da yawa a cikin wannan gari suna zaune ne a karkashin bishiyoyi.

XS
SM
MD
LG