Accessibility links

Hukumar kare hakkin bil adama tana kira ga hukumomin Najeriya da kuma kungiyoyin addini, da masu zaman kansu, su taimaka wajen yaki da yawan fyade.

Babbar sakatare a kungiyar kare hakkin bil adama musamman akan muradun mata a Najeriya da ake kira WRAPA, Hajiya Saudatu Mahdi, inda ta kirayi jama’a akan su kara jajircewa kan fallasa masu irin wannan mummunan aiki.

Hajiya Saudatu tace “a fahimtarmu, abinda ya kamata ayi, sahu da yawa ne. Sahun farko ita kanta al-umma, kamar yadda yanzu muka ga alumma ta jajirce, ana mimmikewa, ana nuna fusata, har in an samu irin wannan. Akwai inda aka samu irin wannan, da kyar aka karbe shi, mutane sun kusa kashe shi. Yarinyar ‘yar shekara uku ce, da ‘yarta mai shekaru hudu. Jajircewar da alumma suka yi, ta taimaka ainun, kuma ya kamata a kara kaimu, abunda turawa suke cewa “zero telorence” wato kada a yarda”.

“Na biyu, kuma ita kanta hukuma, a da gaskiya akwai rauni. Har yau wannan raunin yana nan. Kaga idan kaje kamar wajen ‘yan sanda ka kai karar fyade, yana da wuya kai tsaye a tashi a bincike lamarin”, a cewar Hajiya Saudatu.
Mrs. Mahdi ta cigaba da cewa “idan kaje asibitocin, kafin a karbe ka da irin wannan abun, da irin tambayoyin da ake maka, idan kaje Kotu, kanshi irin tambayoyin da lauyoyin suke yi, ko kuma yadda za’a nemi yarinyar ta tabbatar da abunda aka yi mata, wato sai ta tabbatar da kawo wanda ya gani ana yi mata, babu wanda zai ce kazo kaga abunda ake yi”.

A karshe Hajiya Saudatu Mahadi ta bada shawara.

“Idan ka duba gaba daya, abunda ya cancanta ayi shine a hada kai, a amince a kira gwamnati, dole tayi dokoki kuma jami’ai suyi aiki yadda ya kamata. Alumma suyi gudunmuwa. Duk wanda aka sani yana irin wannan abu, a tona mishi asiri. Mu kanmu iyaye, muma muna da namu. Akwai sakaci, sai kaga yarinya karama an dora mata talla, ko aike ta a lokacin da bai kamata ba”.

XS
SM
MD
LG