Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ma’aikatan gwamnatin Afrika ta Kudu na shirin soma yajin aiki


Ma’aikatan gwamnati a Afirka ta Kudu sun yi watsi da tayin sabon albashin da gwamnatin kasar tayi masu, suka ce za su fara yajin aiki daga gobe Laraba.

Ma’aikatan gwamnati a Afirka ta Kudu sun yi watsi da tayin baya-bayan nan na sabon albashin da gwamnatin kasar tayi masu, suka ce za su fara yajin aikin “sai Baba ta gani” daga gobe Laraba. Gamayyar kungiyoyin ma’aikatan na wakiltar ma’aikata miliyan 1.3 da su ka hada da malaman makaranta, da ma’aikatan asibiti da ‘yan sanda da sauran ma’aikatan gwamnati. Kungiyoyin ma’aikatan dai na bukatar kari ne na kasha 8.6% a albashi wanda hakan ya ribanya yawan faduwar darajar kudin kasar, banda hakan kuma suna bukatar karin kudaden alawus na gidaje. Bayan tattaunawar da aka yi ran Alhamis ne, gwamnatin ta dora kan karin kudaden alawus din da ta yi tayi wa ma’aikatan daga $87 zuwa $95 a wata. To amman tayin karin albashin jami’an na gwamnati zai tsaya a kashi 7%.

XS
SM
MD
LG