Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mutumin Da Ya Bindige Yan Sanda A Garin Dallas


Micah Johnson

Jami’an tsaro sun bayyana sunan mutumin da ake zargi da aikata wannan aika aika da suna Micah Xavier Johnson, daga garin Mesquite dake Dallas. An dai kashe shi ne bayan takaddama da ‘yan sanda a yau Juma’a.

‘yan sanda biyar ne suka rasa rayukansu wasu bakwai kuma sun raunata a harin kwantan baunar da aka kai musu, wanda ya faru ne a yayin wata zanga zangar nuna rashin jin dadin kashe bakaken fata da ‘yan sanda sukayi.

Haka kuma wasu fararen hula biyu sun raunata, a mummunan harin kan jami’an tsaro tun harin ta’addanci da aka kai na 9 ga watan Satumbar shekara ta 2001.

Johnson ya fadawa yan sanda cewa ransa ya baci kan kisan bakaken fata da wasu ‘yan sanda farar fata sukayi, kuma yace yanason ya kashe fararen fata musammanma ‘yan sanda. Haka kuma yace shi kadai ne baya tare da kowacce irin kungiya.

Bayan an dauke sa’o’i ana ja in ja, yan sandan sunyi amfani da wani mutum mutumi mai dauke da bom wajen kashe Johnson.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG