Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Tsohon Firaministan Japan Shinzo Abe


Tsohon Firaministan Japan, Shinzo Abe.
Tsohon Firaministan Japan, Shinzo Abe.

An harbi Abe ta baya, mintina kadan bayan da ya fara jawabi a wajen wani kamfen a ranar Juma’a a yankin Nara da ke yammacin kasar.

Gidan talabijin din kasar Japan na NKH, ya ce tsohon Firaministan kasar Shinzo Abe ya mutu bayan da aka harbe shi yayin da yake jawabi a wajen wani kamfen.

An harbi Abe ta baya, mintina kadan bayan da ya fara jawabi a wajen gangamin a ranar Juma’a a yankin Nara da ke yammacin kasar ta Japan kamar yadda kamfanin dillancin labaran AP ya ruwaito.

An garzaya da shi asibiti ta jirgin sama, amma an gano cewa ba ya numfashi kuma zuciyarsa ta dena bugawa yayin da aka isa wajen likitoci.

Daga baya jami’an asibitin da aka kai shi sun ayyana cewa ya riga ya mutu.

‘Yan sanda sun kama wani dan bindiga a wajen da aka harbe Abe.

“Na rasa abin da zan ce game da rasuwar Abe.

“Wannan harin tsananin mugunta ne da ya faru a daidai lokacin zabe – wanda shi ne ginshikin tsarin dimokradiyyarmu – kuma ba za mu taba lamunta ba.” Firaminista Fumio Kishida da ya gaji Abe ya ce kamar yadda Reuters ya ruwaito.

Wannan lamari dai ya girgigza al’umar kasar ta Japan da duniya baki daya, duba da cewa ana kallon kasar a matsayin daya daga cikin kasashen da ba a tashin hankali.

XS
SM
MD
LG