Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhimmancin Karfafa Dangantakar Soji Tsakanin Amurka Da Japan


Shugaba Donald Trump Da Firai Ministan Japan Shinzo Abe

An jadadda muhimmancin Karfafa dangantakar soji tsakanin Amurka da Japan, ganin irin yadda China ke ta kara zabura.

A daidai lokacinda shugaban Amurka Donald Trump ke kammala ziyarar kwannaki hudu a kasar Japan, an jadadda muhimmancin Karfafa dangantakar soji tsakanin Amurka da Japan, ganin irin yadda China ke ta kara zabura.

A safiyar yau firai Ministan Japan Shinzo Abe, ya shirya wa shugaba Trump liyafa a cikin wani jirgin ruwa mai suna JS Kiga dake jigilar jirage masu saukar ungulu .

Shuwagabannin biyu basu ambaci kasar China ba, koda yake hankalin su yana kan Beijing din ne, akan matsayinta na soji a yankin.

Shugaba Abe yayi magana akan inganata tsaro a yankin.

Shi kuwa Trump cewa yayi idan Japan zata sayi Karin jirgin yaki kirar F-35 guda 105, akan kudi dala miliyan $100 kowanne jirgi daya, hakan zai taimakawa kasashen wajen kare kansu da ma sauran kasashe.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG