Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Dan Jaridar Rasha A Kasar Ukraine


Arkady Babchenko- dan jaridar Rasha da aka kashe a Ukraine

Yan sanda a babban birnin Ukraine Kyiv sun ce an harbe aka kashe wani dan jaridar kasar Rasha Arkady Babchenko da ya arce daga kasarsa a kan abinda ya kira tsangwamar siyasa har lahira, kisar da Firayi Ministan Ukraine ya zargi Moscow da aikatawa.

An harbi Babchenko a bayansa a kofar gidan da yake zaune a Kyiv a ranar Talata, bayan ya dawo cefane kayan abincinsa, a cewar hukumomin Ukraine.

Abokan aikin dan jaridar mai shekaru 41 da haifuwa, sun bayyana kaduwarsu ga kuma hakan ya kara tankiya tsakanin Rasha da Ukraine wanda alakarsu ta riga tayi tsami sakamakon kwace yankin Crimea da Rasha tayi da kuma marawa yan bindigar yan aware a cikin wani mummunan yaki a gabashin Ukraine.

A wani sakon da ya aike ta shafin na Facebook jim kadan bayan labarin mutuwar Babchenko, Firayi ministan Ukraine Volodymyr Hroysman yace yayi imani gwamnatin Rasha ba zata yafe masa ba a kan son gaskiyarsa da da matsayinsa na neman adalci.

Amma a can Moscow, kwamitin binciken Rasha ta nesanta fadar Kremlin da wannan kisan, yana mai cewar ya kaddamar da bincikensa a kan mutuwar Babchenko.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG