Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Amurka An Kashe Wasu Mutane Sanadiyar Kare Wata Musulma


Wasu mutane biyu sun gamu da ajaliinsu a lokacin da suke kokarin kare wata mata muslma

A Amurka, yanzu haka wasu mutane biyu dake tafiya tareda sauran fasinjoji akan wani jirgin kasa a jihar Oregon, sun mutu, sannan akwai wani mutum na ukku dake kwance a assibiti cikin mummunan hali, duk bayanda suka yi kokarin shiga tsakani sadda suka ga wani mutum yana ta cilla asshar akan wasu mata biyu wadanda, bisa dukkan alamu, Musulmi ne, musamman da yake daya daga cikinsu tana sanye da Hijab.

Shi mutumen da ya nemi cin mutuncin matan, wanda ya dauko wuka, ya shiga sukar sauran mutanen dake cikin jirgin, yanzu haka yana hannun ‘yansanda, har an bada sunansa da cewa ana kiransa Jeremy Joseph Christian, 35, dan garin Portland wanda ashe ma ya taba zama fursuna a gidan wakafi.

A nan cikin jirgin dai Christian ya soki mutane ukku ne, daya ya mutu nan take a cikin jirgin, na biyu a assibiti, na ukkun kuma ana kulawa da shi a wata assibitin.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG