Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kawo Karshen Barkewar Cutar Amai Da Gudawa a Sudan ta Kudu


Kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na MDD, Fillipo Grandi yana ganawa da 'yan gudun hijran Sudan ta Kudu a lokaicn da suka isa Uganda. Janaiaru. 30, 2018. (H. Athumani/VOA)
Kwamishinan kula da 'yan gudun hijira na MDD, Fillipo Grandi yana ganawa da 'yan gudun hijran Sudan ta Kudu a lokaicn da suka isa Uganda. Janaiaru. 30, 2018. (H. Athumani/VOA)

An kawo karshen matsalar barkewar cutar amai da gudawa a Sudan ta Kudu, a cewar hukumar lafiya ta duniya, WHO.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO ta ce an kawo karshen matsalar barkewar cutar amai da gudawa ko kuma Cholera, da ta hallaka mutane 400 a kasar.

Hukumar ta lafiya tare da hadin kan jami’an ma’aikatar lafiyar kasar ta Sudan ta Kudu ne suka bayyana kawo karshen cutar a wani taron manema labarai da aka yi a Juba.

Barkewar cutar, wacce ita ce mafi girma a tarihin kasar, ta faro ne daga tsakiyar shekara 2016 a daidai lokacin da sabon fada ya barke a Juba.

Ministan kiwon lafiya a kasar ta Sudan ta Kudu, Riek Gai Kok, ya ce, cikin makwanni bakwai da suka gabata, ba a sake samun wani da ya kamu da cutar ba a duk fadin kasar, amma ya ce, hakan ba ya nufin mutane su yi sakaci bane.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG