Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Sahel Sun Dukufa Wajen Ceto Tafkin Chadi Da Kogin Niger


Taron kwamitin yaki da fari a yankin Sahel

Kasashen yankin Sahel sun amince da yin anfani da makamashin iskar gas da rana da kuma ceto kogunan Chadi da Niger da zimmar bunkasa rayuwa da tattalin arzikin kasashen yankin 13.

Kwamitin kasashen yankin Sahel ya yanke shawarar hanzarta ayyukan ceto Tafkin Chadi da Kogin Niger daga mawuyacin halin da suke ciki.

A dauki wannan matsaya ce domin al'ummar yankin zsu amfana da albarkatun da Allah ya yankin.

Ministan bunkasa ayyukan noma da kiwo a Niger, Alhaji Albade Abuba, ya ce kogin tafkin Chadi kasa ta fara cika shi dalili ke nan da shugabannin suka ba da umurnin a nemi hanyar da za'a ceto kogin tun yanzu.

A cewarsa, haka ma kasa ke yi wa Kogin Niger barazana yana mai cewa asarar wadannan kogunan zai sa rayuwa a yankin ta yi wuya.

Shugaban kasar Burkina Faso Kabore da ke karban shugabancin kwamitin kasashen daga shugaban kasar Mali Bubakar Keita ya gargadi kasashen su gaggauta biyan kudaden karo-karon da ya wajaba a kansu domin a samu a gudanar da ayyukan kungiyar kamar yadda ya kamata.

Saurari rahoton Sule Mumuni Barma domin karin bayani:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG