Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mozambique Ta Musanta Yin Kasuwanci Da Korea ta Arewa


José Pacheco, ministan harkokin wajen kasar Mozambique
José Pacheco, ministan harkokin wajen kasar Mozambique

Kasar Mozambique ta na musanta zargin da ake yi mata na cewa ta na ci gaba da huldar kasuwanci da Korea ta Arewa wanda hakan ya saba takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta saka wa Korea ta Arewan.

Wani rahoton gidan talabijin din CNN da aka wallafa wannan watan ya gano cewa Korea ta Arewa ta sanya hannu kan wasu kwangiloli na miliyoyin daloli a Mozambique.

Bayanai sun yi nuni da cewa Korea ta Arewan ta yi amfani da ribar da ta samu daga sana’ar kamun kifi a gabar tekun Mozambique wajen tafiyar da shirin makaman Nukiliyarta.

Amma mataimakiyar Ministar harkokin wajen Mozambique, Maria Manuela Lucas, ta musanta zargin cewa gwamnatin Mozambique ta yi wata yarjejeniya da Koriya ta arewa wadda ta sabawa takunkumin Majalisar Dinkin Duniya.

Ta kuma ce kasar na maraba da duk wasu masu ido da za su kai ziyara kasar domin tantance gaskiyar lamarin.

Ms. Lucas ta ce kwanan nan gwamnatin Mozambique ta gayyaci kwamitin Majalisar Dinkin Duniya zuwa Mozambique don ganin ayyukan da kasar ke yi da nufin hada kai da akwamitin.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG