Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kawo Karshen Rufe Ma'aikatun Gwamnatin Amurka


Ginin Majalisun Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu a dokar sake bude gwamnati, dake kawo karshen kwanaki uku da aka rufe wasu ma’aikatun gwamnati biyo bayan takaddamar banbancin ra’ayin siyasa kan batun shige da fice.

Da yammacin jiya Litinin ne ‘yan Majalisun wakilai suka kada kuri’a don amincewa da kudurin da Majalisar Dattawa ta amince.

Shi dai wannan kuduri na wucin gadi da aka amince da shi zai baiwa gwamnati kudaden da zata ci gaba da gudanar da harkokinta har zuwa ranar 8 ga watan Fabarairu, da fatan cewa Majalisa zata cimma yarjejeniyar kasafin kudin da bana wucin gadi ba.

Da yake magana da manema labarai Sanata Sherrod Brown na jam’iyyar Democrat, ya ce “wannan labari ne mai kyau ga ‘kasa.”

Sanata Susan Collins ta jam’iyyar Republican cewa ta yi, “yau ranace da za ayi farin ciki. Idan aka rufe gwamnati, hakan na nuna gazawa.”

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG