Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mata Sun Gudanar Da Babban Gangami a Fadin Amurka


Daruruwan mata sun yi zanga zangar nuna bacin ransu ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump a sassa daban-daban na kasar, inda suka sha alwashin ci gaba da adawa da manufofin sa.

Magajin garin birnin New York na Amurka, Bill deBlasio, ya ce masu zanga-zanga sama da 120,000 ne suka halarci gangamin neman ‘yancin mata a unguwar Manhattan, yayin da sauran dubban mutane kuma suka yi zanga-zangar a sauran birane a fadin kasar.

Ranar gangamin mata na wannan shekarar yazo ne daidai da zagayowar hawan shguaban Amurka Donald Trump bisa gadon mulki, kuma yawancin mutanen da suka gudanar da zanga-zangar jiya Asabar sun nuna bacin ransu da Donald Trump a sakonnin da suke dauke da su a kwalaye da kuma tufafinsu.

New York Women's March
New York Women's March

Matan sun hadu ne domin kira ga a baiwa mata ‘yanci daidai dana maza ta fuskar biyan albashi da kuma harkokin kiwon lafiya, sun kuma yi Allah wadai da yawan son yin lalata da mata ala tilas, da kuma karfafawa mata gwiwa su tsaya takarar siyasa.

Haka kuma gangamin ya tabo batutuwa da suka hada da nuna banbancin launin fata da takaita mallakar bindigogi da kare baki.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG