Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kusa Fara Aikin Gyaran Matatun Mai Na Kaduna, Warri - Kyari


Alh Mele Kyari

Shugaban kamfanin man fetur na Najeriya NNPC Malam Mele Kyari ya ce nan ba da himawan ba za a fara gyaran matatun mai na Kaduna da Warri a wani yunkuri na samar da wadataccen mai a kasar.

Yayin wata hira ta musamman da ya yi da Muryar Amurka, Kyari ya ce Najeriya ta hada kai da kasar Rasha a kokarin da take yi na ganin ta gudanar da gyaran wadannan matatun man.

"Najeriya tana bukatar mai da yawa, don wadatar da 'yan kasa, don haka ko da an kammala gyaran wadannan matatun ba za su wadatar da kasar ba, Abin da Najeriya ke bukata ya haura ganga miliyan hamsin."

Alh. Mele Kyari, lokacin ziya a matatar Mai
Alh. Mele Kyari, lokacin ziya a matatar Mai

A dalilin haka ya ce akwai bukatar masu hannu da shuni a kasar su tashi tsaye wajen saka jari don kafa matatun mai masu zaman kansu, kamar yadda Dangote ya fara, idan aka samun yawaitar wadannan za'a iya samun saukin karancin mai a Najeriya.

Matatun man na Kaduna da Warri sun Jima ba sa aiki.

Alh. Mele Kyari, Tare da wakilan kasashen waje
Alh. Mele Kyari, Tare da wakilan kasashen waje

Shugaban kamfanin na NNPC ya kuma shaidawa Muryar Amurka cewar, "a shekarun baya an tafka kura-kurai, yanzu suna aikin gyaran kura-kuran, irin yadda ba'a nazarci yadda matatun man ke aiki ba da kuma irin adadin da za su iya samarwa."

Sai ya kara da cewar "ba za'a ce abin kunya ba ne ga kasa irin Najeriya mai arzikin mai ta koma tana shigo da mai daga kasashen ketare ba. Amma abin da ya sani shi ne, idan ka yi kuskure to babu laifi idan ka dauki laifinka don neman hanyar gyara, wanda yanzu haka shi suka sa a gaba."

Ga cikakkiyar hirar da suka yi da Yusuf Aliyu Harande.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
XS
SM
MD
LG