Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Wawashe Runbunan Gwamnati Da Na Dangote a Jihar Kogi


Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello.

Gwamnatin jihar Kogi ta ce ta tafka asarar miliyoyin Naira sakamakon wawashe kayan abinci da kaddarorin gwamnatin jihar da aka yi a ma’ajiya.

Bayanai sun nuna cewa an samu asarar rayuka lokacin da dubban mutane suka afkawa runbun adana abinci na gwamnatin jihar Kogi. Shedun gani da ido sun bayyana yadda cunkoson mutane cikin runbun ya haddasa tsananin zafi da ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku.

Kwamishinan labarai na jihar Kogi, Mista Kensly Pamwo ya ce abin takaici ne yadda aka lalata kaddarori na miliyoyin Naira daga wasu zauna gari banza da aka dauki nauyinsu.

A jihar Neja, ranar Talata an fasa rumbunan ajiyar wasu yan kasuwa ciki har da na kamfanin Dangote dake garin Suleja, kamar Yadda shugaban hukumar bada agajin gaggawa na Jihar Neja, Alhaji Ibrahim ya tabbatar.

Masu sharhi dai sun ce jama’a sun fara wuce gona da iri dan haka akwai bukatar daukar mataki kamar yadda daya daga cikinsu malam Yusuf Ladan ya bayyanawa Muryar Amurka.

A halin da ake ciki dai, rundunar yan sandan jihar Neja ta ce ta kama wasu matasa 17 da suka shirya gudanar da wata zanga-zanga ba tare da izinin gwamnati ba.

Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:55 0:00


Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG