Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Labaran Kanzon-Kurege Na Barazana Ga Zaman Lafiya A Najeriya - Lai Mohammed


Alhaji Lai Mohammed
Alhaji Lai Mohammed

A cigaba da cece kuce da kuma bayar da ba'asi da ake yi game da zanga zangar SARS da abubuwan da su ka biyo baya, Ministan Yada Labaran Nijeriya ya ce ba wani cigaba da za a samu muddun ba a yi watsi da labaran karya ba.

Ministan Yada Labarai da Al’adu Na Najeriya, Alh. Lai Mohammed, ya ce kasar na zaune ne akan bam wanda ke shirin tashi cikin kankanin lokaci, saboda irin labaran kanzon kurege da ke yawo a kafafen sadarwar zamani.

Ministan yayi wadannan kalaman ne a lokacin da yake kare kasafin kudi na ma’aikatarsa a gaban kwamitin majalisar tarayya. Ya kara da cewar “Muna zaune akan babbar matsala wadda ta shafi labaran karya a kasar nan, kuma bamu da wasu dokoki masu tsauri akan hakan.”

“Haka idan muka je kasar China, bamu samun dammar bude shafukan mu na Facebook, Google ko Instagram, kai wani lokaci ma bama iya bude runbun ajiyar bayananmu na sakon email, saboda dokokinsu.” Suna da tsare-tsare masu kyau a bangaren amfani da kafafen sadarwar zamani.

Idan ba a manta ba a watan Yunin shekarar nan a kasar Habasha an gudanar da zanga-zanga akan kisan wani mawaki, wanda gwamnatin kasar ta umurci da a rufe duk wasu kafafen sadarwar zamani, har na tsawon kwanaki biyu.

Muna da bukatar habaka kimiyya da fasahar zamani da kudade don mallakar kafafen sadarwar zamani, haka zalika sai mun samar da dokokin da zasu bayyana irin labaran da zamu iya sakawa da wadanda ba za mu iya sakawa ba.

Har sai da kasar ta samu kanta sannan aka bude kafofin, duk kuwa da cewar ana gudanar da taron kasashen kungiyar Afrika a kasar. Lai, ya kara da cewar “Abu mafi a’ala shine a rufe duk wasu kafafen sadarwar zamani.”

Ya ce "Babban kalubale da kasar ke fuskanta shine na labaran karya da yadda ake juya labarai daga yadda suke tun asali, zuwa son rai na mutum."

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG