Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kushewa Matakin Birtaniya Da Faransa Na Kifar Da Gwamnatin Moammar Gaddafi


 Muammar Gaddafi
Muammar Gaddafi

Wasu wakilan majalisar dokokin Birtaniya sun kushewa matakin da Birtaniya da kuma Faransa suka dauka a shekara ta Dubu Biyu da Goma sha Daya da ya kai ga kifar da gwamnatin shugaban Libya Moammar Gaddafi.

Rahoton kwamitin musamman na Majalisar Birtaniya kan harkokin kasashen waje, yace rashin yin kyakyawan shiri bisa la’akari da abubuwan da zasu biyo baya , yana nufin Libya zata fada cikin rudani, inda abokan adawa suka shiga neman mulki kungiyar ta’addanci ta IS kuma tana kara samun mafaka a kasar.
A nan Washington ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta kara jadada cewa gibin da aka samu na shugabanci shine yayi dalilin rigingimun biyo bayan faduwar Gadhafi.


Mukkadashin kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Mark Toner, ya fada a jiya Alhamis cewa, sun gano ba a gaggauta daukar matakan da suka dace ba, bayan kawar da Gadhafi wanda zai taimakawa sabuwar gwamnatin kasar ta tsaya sosai tayi aiki.


Wannan hukunci mai gauni, ya zo ne bayan shekaru biyar da tsohon Fara Ministan Birtaniya na waccan lokaci David Cameron da tsohon shugaban Faransa na lokacin Nicolas Sarkozy suka bayyana a Liberty Square a birnin Benghazi a cikin watan Satumba a matsayin masu galaba, inda dubban mutane suka yi ta Shewa . Farmakin hadin guiwansu ta sama da makamai masu lizzami sune suka yi sanadiyar hambarar da gwamnatin Gadhafi dan mulkin mallaka.

XS
SM
MD
LG