Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Sudan Ta Kudu Ta Karyata Cewa Tana Wawure Dukiyar Kasar


Wani mai magana da yawun Shugaban Sudan Ta Kudu, Salva Kiir, ya yi watsi da rahoton wani bincike wanda ya zargi Kiir da tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Riek Machar, da wawurar dinbin dukiyar kasar, yayin da miliyoyin 'yan Sudan Ta Kudun ke fama da matukar yinwa.

Kakakin mai suna Ateny Wek Ateny ya fadi jiya Talata cewa rahoton, wanda ya fito daga wata kungiyar raji da ke nan birnin Washington DC mai suna "The Sentry", shirme ne kawai da karya. Ya ce manufar rahoton shine yin zagon kasa ga Shugaba Kiir da kuma zubar masa da mutunci.

"Rahoton na Sentry siyasa ce kawai, saboda rahoton na kunshe da yanke hukunci na shiririta game da almundahana a Sudan Ta Kudu, kuma ana son ayi amfani da shi ne kawai wajen canza gwamati ga wadanda ke hayaniyar neman kawo chanjin gwamnati," abin da ya gaya ma Muryar Amurka kenan a birnin Juba.

Kakakin ya karyata zarge-zargen rahoton da ke nuna cewa da Kiir da wasu daga cikin manyan hafsoshin sojan gwamnatinsa, ciki har da Hafsan-Hafsoshin soji Paul Malong, sun yi amfani da yakin kusan tsawon shekaru ukun, wajen arzuta kansu.

Rahoton ya biyo bayan binciken tsawon shekaru biyu da wata kungiya, wadda wani fitaccen dan wasan fina-finan Hollywood, George Clooney da wani dan rajin kare hakkin dan adam John Prendergast ta gudanar. Rahoton ya ce da Kiir da Machar sun amfana da kwangilolin sayo makaman fada, da sayar da man fetur da kuma hannayen jarin wasu kamfanonin da ke Sudan Ta Kudu.

Rahoton ya yi zargin cewa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Machar -- mai ja da Kiir a yakin basasar Sudan Ta Kudun-- ya mallaki gidajen alatu a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, da kuma Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

XS
SM
MD
LG