Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kwantar Da Lauyar Da Ta Yi Yajin Cin Abinci Na Kwanaki 40 a Asibiti


Lauyar kare hakkin bil Adama dake gidan Yari a Iran, Nasrin Sotoudeh an kwantar da ita a Asibiti bayan da “ta raunana sosai” bayan kwashe kwanaki 40 ta na yajin cin abinci, a cewar mijinta ranar Asabar.

An dauke ta zuwa sashen kulawa da zuciya jim kadan bayan kaita dakin kulawar gaggawa a Asibitin Taleghani na birnin Tehran, Reza Khandan ya fadawa kamfanin dillancin labaru na AFP ta waya.

Sotoudeh ta kasance cikin yajin cin abinci har tsawon sama da kwanaki 40, a cewar Khandan.

Ta fara wannan yajin ne da zummar kira ga a saki fursinonin siyasa, a kuma mayar da hankali kan halin da suke ciki lokacin annobar coronavirus, a cewar wata sanarwar Sotoudeh wadda mijinta ya kafe a shafukan sada zumunta.

Ya zuwa yanzu dai cutar ta kashe sama da mutum 24,000 da kuma kama ‘yan kasar Iran kusan 420,000 bisa ga kididdigar jami’ai.

Khandan ya fadawa AFP cewa ya damu da matarsa kan cewa Asibitin, “ba wuri ne mai amince ba, ga coronavirus” kuma ba a killace wadanda suka kamu da coronavirus.

Sotoudeh mai shekaru 57, an yanke mata hukuncin daurin shekaru 12 a gidan Yarin Evin bayan da ta kare wata mata da aka kama dalilin yin zanga-zangar kin amincewa da dokar saka hijabi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG