Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kwantar Da Osinbajo A Asibiti


Osinbajo, lokacin da ake masa allurar rigakafin cutar COVID-19
Osinbajo, lokacin da ake masa allurar rigakafin cutar COVID-19

Mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce, likitocinsa za su yi karin bayani a nan gaba.

Rahotanni daga Najeriya na cewa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya kwanta a asibiti.

Wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na asali mallakar mataimakin shugaban kasar, ta nuna cewa za a yi wa Osinabjo tiyata saboda wani matsanincin ciwo da yake fama da shi a kafarsa.

“An kwantar da ni a asibiti a yau, inda aka min aiki, saboda wani ciwo da yake yawan damu na a kafa.

“Watakila sanadiyyar wasan kwallon squash na samu raunin.” Takaitacciyar sanarwa ta ce, wacce aka kafe ta da wani jan kwallo a shafin Facebook din mataimakin shugaban kasar a ranar Asabar.

Mai magana da yawun Osinbajo Laolu Akande wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce, likitocinsa za su yi karin bayani a nan gaba.

“Likitocinsa za su yi karin haske kan maganin da ake masa.” Akande ya ce a shafinsa na Twitter.

Sai dai sanarwar ba ta ambaci asibitin da aka kwantar da mataimakin shugaban kasar ba.

Osinbajo, mai shekaru 65, ya zama mataimakin shugaban kasa ne a shekarar 2015 bayan da suka lashe zabe tare da Shugaba Muhammadu Buhari.

XS
SM
MD
LG