Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Osinbanjo Ya Bar Jam'iyar APC Reshen Jihar Legas


Yemi Osibanjo
Yemi Osibanjo

Kwanaki biyu bayan da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya ayyana bukatarsa ta neman takaran shugabancin Najeriya a karkashin tutar jam'iyarsu ta APC mai mulki. Ofishin mataimakin shugaban kasa ta ce ya sauya mazabarsa daga jihar Legas zuwa jihar Ogun. 

Wata sanarwa da kakakin mataimakin shugaban kasar Mr. Laolu Akande ya fitar na cewa tun a ranar 9 ga watan Janairun shekarar 2021 ne Osinbajo ya sauya mazabarsa da kuma zama mamba na jam'iyar ta APC daga Legas zuwa jiharsa ta asali wato Ogun duk dai a yankin Kudu maso yanmacin ta Najeriya.

Tuni dai masu lura da harkokin siyasar kasar suka ce ba su yi mamakin wannan mataki ba, ganin yarda dama siyasar jihar Legas ke hannun jagorancin wanda ake ganin uban gidan siyasar Osinbajo ne, wato tsohon gwamnan jihar Legas Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

A 'yan makonnin da suka gabata, shi ma Tinubu ya ayyana bukatar neman takarar shugabancin kasar.

Matakin na mataimakin shugaban kasar na kauracewa Legas dai, ana ganin wata dabara ce ta kaucewa adawar da zai fuskanta a karkashin 'ya'yan jam'iyar ta APC a jihar Legas wajen zaben fidda gwani.

Tuni dai jamiyar APC reshen jihar Legas ta ce ta yanke shawarar wanda za ta marawa baya a wannan zabe mai zuwa, wanda kuma bai wuce Bola Tinubu ba.

Jam'iyar ta APC reshen jihar Legas ta yi wani gugar zana ga mataimakin shugaban kasar, inda ta ce ba shi da tasiri a siyasar yankin balle na kasa, hasali ma ko akwatin kofar gidansa bai taba kawo wa APC ba a Legas.

"Wannan alamu ne na gazawa, wanda dama ba mu yi mamaki ba domin (Osinbajo) ba shi da tasirin siyasa a jihar Legas, balle yankin Yarbawa koma Najeriya. " Wani mazaunin Legas ya fadawa Muryar Amurka.

Ko da yake kokarin jin ta bakin kakakin Yemi Osinbajo ya ci tura wani mai goyon bayansa na ganin matakin daya daukan ya dace a wannan tafiya da ya yi kama da na gudun yada kanin wani, kuma a cewar sa za su ci gaba da mara masa baya har sai sun ga abin da ya turewa buzu nadi a wannan tafiya.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:47 0:00
XS
SM
MD
LG