Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Mayar Da Tsohon Lauyan Trump Gidan Yari


Hukumar kula da gidajen yarin Amurka ta ce tshohon lauyan shugaban kasa Donald Trump, Michael Cohen ya koma gidan yarin gwamnatin tarayya bayan ya ki amincewa da ka’idoji na karasa wa’adinsa a gida.

An yakewa Cohen hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara uku saboda an same shi da laifin kin biyan haraji, yin karya ga ‘yan majalisa a kan aikin ginin Trump a Moscow, da kuma biyan wasu mata biyu kudi don su rufe bakinsu aan zargin yin lalata da suka yi ikirarin yi tare da Trump kafin ya zama shugaban kasa.

An sake shi ne daga gidan yari a watan Mayu saboda annobar coronavirus inda aka ba shi umarnin ya karasa shekara daya da rabin da ya rage masa a gidansa na New York.

Amma a jiya Alhamis mai shari’a ya umarce shi da ya koma gidan yarin tarayya bayan da lauyan Cohen, Jeffrey Levine, ya kalubanaci ka’idojin da aka gindaya masa na karasa sauran wa’adinsa a gida.

Ka’idojin sun hada da umarnin da ya hana Cohen yin hulda da kafafan yada labarai da kuma wallafa abubuwa a kafafan sada zumunta.

Levine ya ce jami’an tsaron Amurka sun saka wa Cohen ankwa kafin su tisa keyarsa zuwa gidan yarin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG