Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nada Atiku Abubakwar Wazirin Adamawa


Atiku Abubakar Sabon Wazirin Adamawa
Atiku Abubakar Sabon Wazirin Adamawa

Dubban jama’a sun halarci bikin nadin Wazirin Adamawa Atiku Abubakar, ciki har da tsoffin shugabannin Najeriya da gwamnoni da kuma sarakunan gargajiya

Cikin manyan bakin da suka halarci bikin nadin akwai tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo da Dakta Goodluck Jonathan. A takaitaccen jawabinsa, Obasanjo ya bayyana muhimmancin masarautu ga ci gaban kasa, wanda ya ce Najeriya na bukatar mutanen da za su kawo mata hadin kai.

Obasanjo, wanda ya tabbatar da cewa babu batun rashin fahimtar juna a tsakaninsa da tsohon mataimakinsa Atiku Abubakar, ya bukaci sabon Wazirin Adamawa da ya yi amfani da wannan mukamin na sa wajen da ga martabar masarautar.

Da yake nadin, lamidon Adamawa Dr Muhammadu Barkindo Aliyu Mustapha, shugaban Majalisar sarakunan jihar, ya fadawa Atiku cewa wannan mukami ne da ke zama na biyu a Majalisar masarautar, biyo bayan irin gudumawar da Atikun ya kawo a jihar da kuma arewa maso gabashin Najeriya, da suka hada da kafa jami’a da kuma kamfanonin dake samar da aikin yi ga al’umma.

Bayan an yi nadin, Atiku Abubakar wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na babbar jam’iyar adawa a Najeriya, PDP, ya yaba da tsarin ilimi na zamanin NA har zuwa na lardi wanda su suka ba shi damar karatun da yayi duk da cewa yana dan talaka.

Da yake jawabinsa Wazirin, ya ce “Wannan tsari su suka samar min da dama da har na yi karatu ina dan talaka. Godiya ga masarautun mu, kuma zamu yi aiki tukuru don kawo ci gaba.”

Kamar yadda alkalumman tarihin masarautar ke nunawa Atiku Abubakar shine Waziri na bakwai, yayin da dansa kuma yanzu ya zama Turakin Adamawa.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG