Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anambra: Yan Awaren Biyafara Sun Kashe Wani Dan Sanda, Sun Kuma Raunata Wasu Biyu, a Nnewi.


Shugaba Muhammadu Buhari

kungiyar tsagerun 'yan awaren biyafara sun far wa 'yan sanda inda suka kashe wani sufeto, baya ga raunata wasu 'yan sandan biyu, ciki har da shugaban 'yan sandan yankin Nnewi dake jihar Anambra

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce jami'anta a Nnewi, Jihar Anambra da ke kudu maso gabashin kasar, ta kama wasu mutane kimanin 34 'yan kungiyar tsagerun 'yan aware ta Biyafara wato (IPOB) ta 'yan kabilar Igbo zalla da ke kokarin ballewa daga Najeriya.

Rundunar ta ce jami'anta, tun da farko, sun sami bayanan sirri da ke nuna cewa tsagerun 'yan awaren da dama sun tattaru a wani yanki da ke cikin garin Nnewi inda su ke kokarin tayar da hankali, al'amarin da ya sa kwamandan 'yan sandan yankin ya jagoranci sauran jami'ansa don samar da tsaro.

Bayan jami'an 'yan sandan sun isa gurin ne kuma sai 'yan awaren su ka abka masu, inda su ka kashe sufeton dan sanda da ji wa wasu karin manyan jami'an 'yan sanda biyu rauni, ciki har da DPO, sannan kuma suka kone motar sintirin 'yan sanda yankin kurmus.

Ga Hassan Maina Kaina da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG