Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Fararen Hula Masu Aikin Tsaro A Borno


Gwamnan Jihar Borno, Kashim Shettima, yana gaisawa da matasa fararen hula masu farautar 'yan Boko Haram, "Civilian JTF" a Maiduguri

An horas, aka ba da aiki ga matasa 632 na "Youth Vanguard" domin su yi aiki tare da jami'an tsaro wajen ci gaba da farautar 'yan Boko Haram

Gwamnatin Jihar Borno, ta bayar da aiki na dindindin ga matasan nan 'yan banga da aka fi sani da sunan "Civilian JTF" wadanda suke taimakawa jama'a da kuma jami'an tsaro wajen farautar 'yan bindiga na kungiyar nan da aka fi sani da sunan Boko Haram.

Da yake magana a wajen rantsar da matasa su 632 wadanda suka kammala horo kan ayyukan tsaro a sansanin horas da matasa masu aikin bautar kasa dake Maiduguri, gwamna Kashim Shettima na Jihar Borno, ya bayyana godiyarsa da ta illahirin al'ummar jihar ga wadannan matasan da suka sadaukar da rayukansu domin farauto wadannan 'yan bindiga, duk da mummunan hatsarin dake tattare da yin hakan.

Yace ba zai iya misalta muhimmancin ayyukan da su wadannan matasa suke gudanarwa ba, a saboda abinda suka yi ma jihar Borno, ba wanda zai iya biyansu.

Su dai wadannan matasa da ake kira "civilian JTF" ko kuma "Youth Vanguard" bullarsu da farko a garin Maiduguri, ita ce ta taimaka fiye da matakan da dakarun gwamnati suek dauka, wajen zakulo 'ya'yan kungiyar Boko Haram tare da hana su samun wurin fakewa a unguwannin da a can baya suka zamo tungayensu a cikin babban birnin na Jihar Borno.

Nan da nan wadannan matasa 'yan banga suka bazu a cikin jihar zuwa sauran yankunan kananan hukumomi da garuruwan da 'yan Boko Haram ke shiga su na buya, su na damko su tare da mika su ga hukumomin tsaro.

A yanzu, matasan da suka samu wannan horo, zasu bazu zuwa garuruwansu, domin gudanar da ayyuka kafada da kafada da jami'an tsaro wajen farautar tsagera.

Haka kuma an dinka musu kayayyaki na musamman wadanda daga gani za a iya gane su.

Wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda, ya aiko da cikakken bayanin wannan daga Maiduguri...
XS
SM
MD
LG