Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Sabon Firai Minista A Spain


Pedro Sanchez yan daukar rantsuwa

An rantsar da shugaban ‘yan gurguzu Pedro Sanchez yau asabar a matsayin sabon Firai Ministan kasar Spain, bayanda majalisar dokokin kasar ta kada kuri’ar nuna rashin goyon bayan Firai Minista Mariano Rajoy jiya Jumma’a.

Sarkin Spain Felipe na shida ne ya rantsar da sabon Firai ministan a wani buki da aka yi a fadarsa dake Zarzuela kusa da Madrid.

Sanchez ya sami nasara ne bayan kada kuri’a kan kudirin da aka gabatar na nuna rashin goyon bayan Pirai Ministan, inda ‘yan majalisa dari da tamanin suka goyi bayan kudurin, yayinda dari da sittin da tara suka nuna rashin goyon baya,dan majalisa guda kuma bai kada kuri’a ba a majalisar wakilai mai kujeru dari uku da hamsin. Wannan ne karon farko da majalisar dokoki ta sauke shugaba a kasar Spain tunda ta kafa mulkin damokaradiya shekaru arba’in da suka shige.

An kada kuri’ar nuna rashin goyon bayan Rajoy ne bayan shekaru shida da hawansa karagar mulki, sakamakon laifin cin hanci da rashawa da ya shafi wadansu tsofaffin membobin jam’iyarsa.

Sanchez, shugaban jam’iyar Workers ta ‘yan gurguzu ya zama Pirai Ministan Spain na bakwai tunda kasar ta koma mulkin damokaradiya cikin shekara ta dubu da dari tara da saba’in, bayan mulkin kama karya na Francisco Franco.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG