Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Jami'ar Kimiyya Ta Jihar Kebbi Don Gudun Tashin Hankali


An fara samun kwanciyar hankali bayan wata hatsaniya da ta barke tsakanin daliban jami'ar kimiya ta kere kere ta jihar Kebbi dake Aliero da kuma mutanen garin.

An samu tashin hankalin sakamakon danyen hukumcin kisan gilla da aka yi wa wani dalibi dan shekarar karshe ga kammala jami'ar a fannin kimiyar harhada sanadarai Sato Biochemistry.

Daliban na jami'ar kimiya da kere kere ta jihar Kebbi sun nuna rashin yardar su ga abinda ya samu dan uwansu wanda ya yi sanadiyar mutuwar sa.

Dalibin mai suna sharfudeen Sale Kanya ya gamu da ajalinsa ne sanadiyar wata tankiya da ta faru tsakaninsa da wani mai sayar da wayar salula, wanda ke bin dalibin kudi naira 3,500 ragowar kudin wayar da ya saya.

Dalibin yace ya tura masa sauran kudin ta bankin sa kuma an tura masa sakon an cire kudin amma mai wayar ya ce shi baiga kudin ba, abin da yasa ya yi masa ihun barawo

Gwamnatin jihar Kebbi ba ta yi kasa a guiwa ba ganin daliban jami'ar sun dauki niyyar zasu afkawa mutanen gari don daukar fansa.

Rundunar 'yan sanda ta jihar a ta bakin kakakin ta DSP Nafi'u Abubakar ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Yanzu dai mahukunta a jami'ar sun sanar da rufe jami'ar har sai an baiwa daliban tabbacin yin adalci akan abinda ya faru.

A saurari rahoto cikin sauti daga Muhammad Nasir:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:32 0:00

Karin bayani akan: Sale Kanya, jihar Kebbi​, Nigeria, da Najeriya.

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG