Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Kasuwar Baje Kolin Kayan Da Aka Hada A Najeriya

Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohmed a lokacin da yake zagaya kasuwar (Facebook/ Min. of information)
Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohmed a lokacin da yake zagaya kasuwar (Facebook/ Min. of information)

Daga cikin kayan da aka baje, har da mota kirar Hyundai Kona mai amfani da wutar lantarki, wacce aka hada sassanta a cikin kasar.

A Najeriya, an rufe kasuwar baje kolin kayayyakin da aka hada su a kasar, kasuwa da ta kwashe kwana biyar tana ci a Abuja babban birnin tarayyar kasar.

An gudanar da taron ne a babban filin taro na Eagle Square inda ‘yan kasuwa manya da kanana da masu sana’o’in hannu, suka baje kolin kayayyakin da suka hada na cikin gida.

Daga cikin kayan da aka baje, har da mota kirar Hyundai Kona mai amfani da wutar lantarki, wacce aka hada sassanta a cikin kasar.

Lai Mohamed a lokacin da yake duba wata mota da aka hada a Najeriya (Facebook/Min. of Information)
Lai Mohamed a lokacin da yake duba wata mota da aka hada a Najeriya (Facebook/Min. of Information)

"Kayayyakin da aka baje cikin kwana biyar da suka ce, dari bisa dari a Najeriya aka hada su. Hakan na nuna irin kwazo da basira da ‘yan kasuwarmu da masu sana’o’inmu ke da su" In ji Ministan yada labarai Alhaji Lai Mohamed yayin jawabin da ya yi a wajen rufe taron.

Baje kolin kayayyakin, na daga cikin tsare-tsare da hukumomin Najeriya suka shirya na yin bikin cikar kasar shekara 60 da samun ‘yancin kai, bikin da za a kwashe daukacin shekarar 2021 ana yin shi.

Sauran kayayyakin da aka baje har da arzikin ma’adinai da ake tonowa a sassan kasar.

XS
SM
MD
LG