Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rufe Makarantu 31 A Jihar Nejan Najeriya Saboda Rashin Tsaro


Gwamnatin jihar Nejan Najeriya ta sanar da rufe wasu makarantu guda 31 saboda matsalar rashin tsaro da ta addabi jihar.

A wani taron manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwar jihar, kwamishinar kula da harkokin ilimin jihar Hajiya Hannatu Jibiril Salihu ta ce daga cikin makarantun kwana guda 56 dake sassan jihar guda 25 kacal ke bude suna aiki a halin yanzu.

Wannan dai yana zuwa ne a daidai lkacin da aka samu canjin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Alhaji Adamu Usman a sakamakon karin girman da ya samu.

Amma kuma kwamishinan kananan hukumomin jihar Nejan Barrista Abdul-Malik Sarkin Daji ya ce suna fatar samun jajirtaccen sabon shugaban ‘yan sandan bayan la’akkari da yadda jihar Nejan ke fama da matsalar kalubale irin na tsaro.

A halin da ake ciki dai har yanzu daliban Islamiyyar Salihu a jihar Nejan na hannun ‘yan fashin daji sama da watanni biyu kenan duk kuwa da Naira miliyan 30 da iyayen yaran suka ce sun kai ma ‘yan fashin a matsayin kudin fansar yaran.

Saurari rahoto cikin sauti daga Mustapha Nasiru Batsari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00


Matsalar Tsaro A Zamfara

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Kamu A Auren Nupawa

Yadda Nupawa Suke Kamun Ango A Bikin Aure
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG