Accessibility links

An Rufe Makarantu Malakar Gwamnati a Jihar Borno Domin Fargaban Hare-hare


Dalibai cikin aji a ranar farko a makaranta.

An rufe makarantu a jihar Borno.

An rufe makarantu firamari da na sakandare malakar gwamnati a jihar Borno,domin fargaban hare-haren da yan bindiga ke kaiwa a jihar ta Borno.

Ko da yake makarantu masu zamman kansu na ci gaba da koyar da dalibainsuma sun rage lokacin karatu da kimanin awowi biyu zuwa hudu.

Daukan wanna mataki ya biyo bayan rahotanin ne na tsaro inji wakilinmu dake jiharta Borno.

Ya kuma kara da cewa babu takamamma lokaci da za'a bude makarantun a yanzu, sai komai ya lafa domin hana afkuwan abinda ya faru a jihar Yobe.

XS
SM
MD
LG