Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Goodluck Jonathan ya Nemi Hadin Kan Makwabta Wajen Yakar Ta'addanci


Shugaba Goodluck Jonathan
Shugaba Goodluck Jonathan

Shugaban yace Boko Haram da sauran masu aikata laifi dake ta'addanci a bakin iyaka, barazana suke yi ga duk makwabtan ba Najeriya kawai ba.

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya yayi rokon da a kara samun hadin kai a tsakanin kasar da makwabtanta a yakin da ake yi da ta'addanci.

Shugaba Jonathan ya furta wannan ne a lokacin da yake karbar sako na musamman daga shugaban kasar Kamaru, Paul Biya, ta hannun wakilinsa na musamman, Emmanuel Sadi Rene.

Kakakin shugaba Jonathan, Reuben Abati, ya ambaci shugaban a cikin wata sanarwa yana cewa kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin masu aikata laifi a yankunan bakin iyaka su na yin barazana ga dukkan kasashen ne.

Yace tilas Najeriya da makwabtanta su dauki matakan gaggawa na hada karfi waje guda domin yakar 'yan Boko Haram da sauran kungiyoyin dake amfani da bakin iyakoki wajen aikata laifuffuka.

Rene, wanda shi ne ministan harkokin cikin gidan Kamaru, ya tabbatarwa da shugaba Jonathan cewa kasarsa zata bayarda cikakken hadin kai ga Najeriya wajen yakar kowane irin ta'addanci.

Har ila yau, yace har abada kasar Kamaru ba zata kyale a yi amfani da yankinta a zaman mafaka ta 'yan ta'adda ba, ko kuma sansani na gurgunta Najeriya.
XS
SM
MD
LG