Accessibility links

Mutanen da Suka Mutu a Harin 'Yan Bindiga a Katsina ya Zarce 100


Gidajen da suka kone bayan hare-haren Boko Haram a bama, Fabrairu 20, 2014.

Yayin da aka kashe dan sanda guda, da farar hula guda da kuma dan bindiga guda lokacin da wasu mahara su hudu kan babura suka yi kokarin fashi a Jihar Kebbi

Adadin mutanen da suka mutu a sanadin wani farmakin da 'yan bindiga suka kai a kananan hukumomin Sabuwa da Faskari a Jihar Katsina, yanzu ya haura 100, yayin da wasu da dama suke jinyar raunukan da suka samu.

Wadannan 'yan bindiga da aka ce sun tafi a jerin gwanon babura masu yawan gaske, sun shafe sa'o'i da yawa su na kai farmaki a kan mutanen garuruwa irinsu Marabar Maigona, Unguwar Rimi, Layin Galadima da 'Yar Doka da Maidaura.

Wani mazaunin garin Marabar Maigona, Ibrahim Ahmadu, yace mutanen sun zo a kan babura suka kewaye garin baki daya, suka rutsa da kowa a ciki su na sara da harbin mutane.

Amma rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta musanta cewa an kashe mutane da yawa haka. Kakakin rundunar, DSP Aminu Abubakar Sadiq, yace yawancin 'yan jarida su na magana ne da wadanda ba su ga abubuwan da suka faru da idanunsu ba, sai wadanda suka ji labari kawai.

Yace babu wanda aka kama, amma ana gudanar da bincike, a bayan da ;'yan bindigar suka gudu zuwa cikin daji.

A garin Argungu a Jihar Kebbi ma, wasu 'yan bindiga su hudu a kan babura sun kai farmaki, suka yi sanadin mutuwar mutane 3, cikinsu har da dan bindiga guda, da dan sanda daya da kuma wani farar hula.

Kakakin 'yan sandan Kebbi, Sufritanda Mohammed D. Mainagge, yace an samu nasarar kama biyu daga cikin wadannan 'yan bindigar da aka ce 'yan fashi ne.

XS
SM
MD
LG