Accessibility links

Faransa Ta Ce An Sace Wani Fada Dan Kasar a Kamaru, Kusa da Kan Iyakar Kamaru da Najeriya


Shugaban Faransa Francois Hollande tareda wani dan kasar da aka sace, da kuma ministan harkokin wajen kasar.

Mahukuntan Faransa sun ce an sace wani dan kasar a kamaru, kusa da kan iyakar Najeriya.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Faransa ta bada Rahoton cewar an sace wani baturen kasar faransa mai wa’azin addini a Arewacin kasar kamaru kusa da kan iyaka da Nigeria.

Rahoton da ma’aikatar harkokin wajen kasar Faransan ta bayar na cewa an sace George Vandenbeusch a daren larabar da ta gabata ne a kusa da garin Koza dake da tazarar kilomita 30 daga kan iyaka.

Mukaddashin babban jami’in harkokin wajen kasar Kamaru Mouhe Kolande ya tabbatar da rahotannin aka samu game da sace babban fadan a yankin kan iyaka. Yace wasu mutane biyu suka sace fadan dan kasar Faransan an kuma sami wata jami’ar mujami’ar da ta ga lokacin da mutanen biyu suka sace fadan, harma ta shaidawa makwabta halin da ake ciki domin su kawo dauki.
XS
SM
MD
LG