Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Kai Hari Cibiyar Kula Da Masu Cutar Ebola a Congo


wata mata na kallon wani sashi da mahara suka kona a wata cibiyar kula da masu cutar Ebola a Congo a Butembo,

An yi nasarar kashe daya daga cikin ‘yan tawayen a lokacin harin, wanda aka kai a wani asibiti da ake kira Katwa.

Wasu ‘yan tawaye dauke da muggan makamai, sun far ma wata cibiyar da ake kula da masu fama da cutar Ebola a kusa da birnin Butembo, da ke Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Harin na zuwa ne sa’o’i bayan da wani hari na daban, da ya yi sanadin mutuwar wani likitin kasar Kamaru da ke taimakawa masu fama da cutar, inji ‘yan sandan kasar.

An yi nasarar kashe daya daga cikin ‘yan tawayen a lokacin harin, wanda aka kai a wani asibiti da ake kira Katwa, inda anan ne ma’aikatan lafiya ke kokarin dakile yaduwar cutar, wacce ta barke a gabashin kasar ta Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo.

Mataimakin Magajin gari, Patrick Kambale, ya ce maharan sun yi kokarin kona cibiyar ne a daren jiya.

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG