Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sake Nada Okonjo-Iweala A Matsayin Shugabar WTO

Shugabar kungiyar cinikayya ta duniya WTO, Dr. Ngozi Okonjo Iweala) a Geneva a ranar 16 Fabrairu, 2024.
Shugabar kungiyar cinikayya ta duniya WTO, Dr. Ngozi Okonjo Iweala) a Geneva a ranar 16 Fabrairu, 2024.

Okonjo-Iweala ita ce mace kuma ‘yar Afirka ta farko da ta fara rike wannan mukami tunda aka kafa kungiyar.

An Sake nada Dr. Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin shugabar Kungiyar Cinikayya ta Duniya WTO a wani sabon wa’adin shekaru hudu.

Wa’adin zai fara ne daga ranar 1 ga watan Satumbar 2025 kamar yadda shafin shafin yanar gizon WTO ya wallafa a ranar Juma’a.

“Matakin ya nuna cikakken amincewa da jagorancin ta na musamman da hangen nesan ta na ci gaban WTO nan gaba.” A cewar shafin na WTO.

An fara aikin sake nadin nata tun a ranar 8 ga Oktoba, 2024, wanda Jakada Petter Ølberg daga kasar Norway, wanda shi ne Shugaban Majalisar Dinkin Duniya, ya jagoranta.

“Tunda babu wani karin dan takara da aka gabatar kafin wa'adin ranar 8 ga Nuwamba ya cika, Dr. Okonjo-Iweala ita ce kaɗai ta tsaya takara.” A cewa Majalisar Kolin kungiyar ta WTO.
An gudanar da wannan mataki cikin tsari da gaskiya, daidai da dokokin WTO kan "Tsare-tsaren Nadin Daraktoci Janar mai lamba (WT/L/509).”

Dr. Okonjo-Iweala wacce ‘yar asalin Najeriya ce, ta fara wa’adinta na farko a ranar 1 ga watan Maris 2021. Ita ce mace ta farko kuma ‘yar Afirka ta farko da ta fara rike wannan mukami

This item is part of

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG