Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki 3 Daga Cikin Mutane 6 Da Aka Kama Bisa Zargin 'Yan Boko Haram Ne


Sojojin Najeriya cikin mota mai sulke a Maiduguri, Jihar Borno lokacin Sallar Azumi.

Shiyya ta 7 ta rundunar sojojin Najeriya mai hedkwata a Maiduguri ta ce wadanda aka saki ba su da wata alaka da ta'addanci kamar yadda wasu kafofin labarai ke fada

Shiyya ta 7 ta rundunonin sojan Najeriya mai hedkwata a Maiduguri, ta ce ta saki mutane 3 daga cikin wasu mutane 6 da aka kama a lokacin da suka komo daga aikin Hajji a babban filin jirgin saman Maiduguri bisa zaton ko su na da alaka da kungiyar Boko Haram.

Kakakin shiyya ta 7 ta sojojin Najeriya, Kyaftin Aliyu Danja, ya fadawa 'yan jarida a Maiduguri cewa wadanda aka saki ba su da wata alaka da ta'addanci kamar yadda wani bangare na kafofin yada labarai ke fada.

Kyaftin Danja ya gaskata labarin cewa jami'an tsaro a filin jirgin saman na Maiduguri sun tsarwe mutane 6 bisa zaton ko su na da wata alaka da kungiyar Boko Haram, suka kuma mika su hannun rundunra sojojin. Amma yace a bayan da suka yi tambayoyi masu yawa ma wadannan mutane suka kuma yi bincike, sun gano cewa mutanen ba 'yan ta'adda ba ne, kuma ba 'ya'yan kungiyar Boko Haram ba ne. Yace an saki uku daga cikinsu, kuma har sun koma gidajensu.

Kakakin shiyyar ta 7 ta sojojin Najeriya yace sauran mutane ukun da suka rage ana ci gaba da yi muu tambayoyi, kuma in har aka gano su na da wata alaka ta kai tsaye ko ba ta kai tsaye ba da ayyukan ta'addanci, to zasu fuskanci fushin shari'a.

A ranar litinin da asuba ne aka kama wadannan mutane 6 a lokacin da wani jirgin alhazai ya komo da su daga kasar Sa'udiyya inda suka gudanar da ikin Hajji na bana.
XS
SM
MD
LG