Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Fursunoni 92 a Neja


Fursunoni

A wani mataki na rage cunkoso a gidajen yari, an sallami wasu fursunoni 92 daga gidajen yari biyu dake Minna a jihar Neja.

Babbar mai shari’a Mariya Zukogi, ita ce ta sallami fursunonin wadanda galibinsu sun dade suna jiran shari’a a daure da kuma masu fama da rashin lafiya, sai kuma wadanda aka yi wa afuwar jeka-gyara-halinka.

Babban magatakardan ma’aikatar shari’a a jihar Neja, Alhaji Muhammad Mamba, ya ce a kowacce shekara babbar mai shari’a ta na zuwa gidajen yari don ganawa da fursunoni musamman ma wadanda suka dade ba tare da an yi musu shari’a ba.

Ta kan duba da kuma bayar da umarnin a bayar da belinsu ko kuma idan suka amsa da laifinsu ta na sa wani alkali ya yanke musu hukunci.

Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:54 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG