Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Madugun 'Yan Adawan Rasha


Alexei Navalny A Wurin Taro

A Rasha 'yan sandan kasar sun saki sanannen shugaban 'yan hamayyar kasar Alexei Navalny tareda daruruwan magoya bayansa da suka tsare.

Jiya Asabar aka kama su lokacinda suka shiga zanga zangar da aka yi Moscow da wasu biranen kasar 90, kan bikin rantsar da Vladimir Putin, domin fara wa'adin iko na hudu a zaman shugaban kasar.


Navalny, ya fada ta shafinsa na Tweeter cewa, an sako shi da safiyar jiya Lahadi.
'Yan mintoci da isarsa dandalin zanga zangar a rana r Asabar 'Yansanda suka kama Navalny tareda wani amininsa Nikolai Lyaskin.


'Yansanda dauke da kulakai da wadanda suke sanye da kayan sarki, suka yi ta kutsawa cikin gungun 'yan zang-zangar galibin su matasa 'yan kasar ta Rasha suna ta kama su.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG