Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sako Hambararren Shugaban Burkina Faso


Hayaki ya rufe sojojin Burkina Faso, Alokacin da masu zanga-zangake kan tituna a Ouagadougou, Burkina Faso,Satumba. 18, 2015.

Shugabannin juyin mulkin Burkina Faso sun ce sun sako tsohon shugaban kasar da aka hambare Micheal Kafando bayan tsare shi na tsawo kwanaki biyu, sai dai basu yi wani bayani dangane da Firai ministan kasar ba wanda shima ake tsare da shi.

Shugabannin juyin mulkin sun fitar da sanarwa yau jumma’a cewa, sun saki Kafando da ministoci biyu da suke tsare da su, domin a zauna lafiya.

Basu yi karin haske a kan Firai Minista Isaac Zida wanda suka kama tare da shugabana kasar ranar Laraba ba.

Birgediya janar Gilbert Diendere, shugaban sabuwar majalisar gudanarwar kasar yayi hira da sashen Faransanci na Muryar Amurka jiya alhamis kwana daya bayanda sojoji suka hambare gwamnatin rikon kwaryar kasar suka kama shugabananinta.

Janar din yace sun yi juyin mulkin ne sabili da akwai alamar tambayar a tsarin siyasar kasar. Yace zai fara tattaunawa da dukan bangarorin siyasa.

Dama anyi shirin gudanar da zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa ranar 11 ga watan Oktoba. Sai dai yanzu babu tabbacin ko za a kiyaye ranar.

Jiya alhamis Fadar white House tayi allawadai da kwace mulkin, ta kuma yi kira da a saki shugaban kasar da Firai ministan ba tare da bata lokaci ba.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG