Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An taka kundin tsarin mulkin kasa A Burkina Faso: Ban Ki-moon


Juyin mulki a Burkina Faso
Juyin mulki a Burkina Faso

Rundunar sojan kasar Burkina Faso tace ta kwace ragamar mulkin kasar kuma har ta nada wani babban hafsan sojan don ya jagoranci sabuwar majalisar mulkin da suka kafa don tafiyarda kasar.

Mutumin da aka nada domin ya jagoranci hukumar da masu juyin ke kira “Majalisar Jaddada Akidar Demokaradiya”, Brig-Janar Gilbert Diendere, tsohon na hannun daman tsohon shugaban Burkina Faso din ne, Blaise Campaore wanda shima boren jama’a na bara ya janyo sanadin hambare shi daga karagar mulkin da ya share shekaru 27 akanta.

A yau ne wani jami’in soja ya fito a cikin telebijin yana bada sanarwar cewa an tumbuke gwamnatin ta Burkina, kuma an cirewa shugaban gwamnatin wucingadi na kasar Michel Kafando rigarsa ta mulki. Kuma har yanzu Kafando din da Firai ministan kasar suna tsare a hannun sojan da suka cafke su lokacinda ake wani taron majalisar ministoci jiya Laraba a can birnin na Ouagadougou.

Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya ta la’anci wannan juyin mulkin inda kuma ta nemi a sako mutanen da aka tsare. Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon yace al’amarin, wanda ya bayyana da cewa “taka kundin tsataka kundin tasrin mulkin kasar ne

Bayanda sojojin dake kula da tsaron fadar shugaban kasar Burkina Faso suka bayyana cewa,sun gudanar da juyin mulki a kasar, wakilinmu na birnin Yamai a Janhuriyar Nijar mai makwabtaka da kasar da Burkina Faso Yusuf Abdullahi ya samu zantawa da shugaban Muryar talaka a Nijar Nassiru Saidu wanda a cikin wannan hirar ya soma da yin kira da kasahen duniya na ganin sun tilassawa sojojin barin mulki.

Ga cikakken bayanin Mal Nassiru

Juyin Mulki a Burkina Faso-1:51"
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:51 0:00
Shiga Kai Tsaye

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG