‘Yan sanda a jihar Anambara sun ce masu garkuwa da mutane sun sako wadannan limaman darikar Katolika, guda biyu da aka yi garkuwa dasu a ranar 24 ga wannan watan na Disamba.
Malam Haruna Muhammad, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ne ya shaidawa Muryar Amurka hakan a wannan hirar: Inda yace suna kokarin ganin sun kama wadanda sukayi garkuwa da mutanen, ya kuma tabbatar da cewar suna binciken mabuyar miyagun mutanen.
Babbar gundumar darikar Katolika ta Onitsha ta shida irin halin jin dadi da suka samu kansu a ciki, game da sako wadannan limaman da ke hidima a karkashinta. Reverend Fada Pius Uche Ukor, shine daraktan yada labaran babbar gundumar ya shaida hakan.
Ya ce, “Wannan ya kara farin cikin a rayuwarsu a wannan lokaci na bukukuwa, da shagalin dake tattare da wannan lokacin. Saboda haka, da farin ciki zamu shiga sabuwar shekara muna godewa Allah domin wannan alfarmar, da kuma cewa sun dawo lami lafiya.”
Za ku iya son wannan ma
-
Maris 30, 2023
Kamala Harris Ta Gana Da Mata ‘Yan Kasuwa Na Kasar Ghana
-
Maris 29, 2023
Zimbabwe Na Duba Yiwuwar Soke Hukuncin Kisa
-
Maris 29, 2023
Rundunar Sojojin Kasar Zimbabwe Ta Nemi Tallafin Najeriya.
Facebook Forum