Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Bullar Cutar Kyandar Biri A Kamaru


Cutar Kyandar biri
Cutar Kyandar biri

Cutar Kyandar biri ta bayyana a kasar Kamaru. Wannan labari ya samu ne daga wata sanarwar hukumar lafiya ta duniya. Inda ta ce a kasashe bakwai aka gano wannan annobar a nahiyar Afirka.

A makon da ya gabata ne Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa cutar kyandar biri ta bayyana a kasashen Afirka bakwai, da suka hada da Kamaru, Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo, Saliyo, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Kongo da Najeriya.

WHO tace sabuwar annobar ta shafi akalla mutane 1393. Ya kuma tabbatar da cewa, mutane 44 sun kamu da cutar a nahiyar Afirka.

Ko da yake cutar kyandar biri ba sabon abu bane a Kamaru, a ranar 18 ga Yuli, 2014, Ministan Ma'aikatan Dabbobi, Kamun Kifi da Masana'antar Dabbobi na kasar ya sanar da Hukumar Kula da Lafiyar Dabbobi ta Duniya cewa, rukunin gwaggwan biri shida sun kamu da cutar. Hakan ya kasance a jihar tsakiya, a cikin karamar hukumar Mbinang a Upper Sanaga.

A hirar ta da Muryar Amurka, Dr Nkollo Alida kwararriyar likita game da wannan cutar ta bayyana cewa, “Cuta ce mai yaduwa sosai kuma da hanzari. Tana yaduwa daga biri zuwa mutum. Kuma daga mutum zuwa mutum. Tana shafar yara kanana da yawa. Cuta ce da muka kusan manta da ita. Amma tana da hatsarin gaske.

Ana gane ta da zazzabi da ƙuraje masu fitowa a jikin majiyyaci kamar marurai. Amma hakan ba shi da alaƙa da cutar kashin kaji. Babu takamamman maganin ta a yanzu. Muna yin magani bisa ga alamun da suke bayyana wa kowane majiyyaci. Ya kamata a yi wa dabbobi allurar rigakafi kuma a guji saduwa da dabbobin da suka mutu ba zato ba tsammani”.

An fara gano cutar a jikin birai ne, a cikin dakin gwaje-gwaje a birnin Copenhagen, a Denmark a cikin 1958, tare da samfurin ɗan adam na farko a shekarar 1970 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.

Saurari cikakken rahoton Mohamed Ladan cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00

XS
SM
MD
LG