Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An sami ci gaba a yaki da zazzabin cizon sauro a nahiyar Afrika


Sauro mai haddasa cutar maleriya
Sauro mai haddasa cutar maleriya

Darektan hukumar lafiya ta duniya na shiyar Afrika Dr. Luis Gomes Sambo ya bayyana cewa an sami ci gaba ainun a Afrika a yaki da zazzabin cizon sauro, sai dai yace akwai bukatar kara kaimi domin dorewar wannan nasarar da aka samu.

Darektan hukumar lafiya ta duniya na shiyar Afrika Dr. Luis Gomes Sambo ya bayyana cewa an sami ci gaba ainun a Afrika a yaki da zazzabin cizon sauro, sai dai yace akwai bukatar kara kaimi domin dorewar wannan nasarar da aka samu.

A cikin sakonshi ma ranar yaki da cutar kanjamau ta duniya cikin shekarar da ta gabata, Dr Sambo yace akwai kwarin gwuiwa ganin yadda ake kokarin shawo kan wannan cutar a duk fadin Afrika. Misali, kafa wannan kungiyar ta shugabannin kasashen nahiyar Afrika dake yaki da zazzabin cizon sauro da ake kira Kungiyar shugabannin kasashen Afrika mai yaki da zazzabin cizon sauro, ko kuma “African Leaders Malaria Alliance” da ake kira ALMA a takaice. Kungiyar ta kuduri aniyar hannu kai wajen yaki da zazzabin cizon sauro da kuma kawar da cutar baki daya, da shawo kan mace mace ta dalilin wannan cutar nan da shekara ta dubu biyu da goma sha biyar.

Ya kuma kara da cewa, kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afrika da kuma kungiyar hadin kan tattalin arzikin yankin suma sun ba yaki da zazzabin cizon sauro fifiko a cikin shirye shiryensu.

Bisa ga cewar Dr. Sambo kasashe da kuma abokan fama a wannan fafatukar suna kokari ainun wajen ganin sun sami ci gaba a yunkurin yaki da zazzabin cizon sauro a yankin. Kasashen da wannan cutar tayi kamari sun sa yaki da zazzabin cizon sauro a tsare tsarensu na yaki da talauci. Ana ci gaba da sake nazarin ayyukan da ake gudanarwa yayinda ake la’akari da kudaden da ake kashewa da kuma gibin dake akwai domin samun damar shawo kan cutar a kasashen duniya baki daya.

Darektan Hukumar lafiya ta Duniya na yankin Afrika Dr. Luis Gomes Sambo ya bayyana cewa, a karshen shekara ta dubu biyu da goma, an sami kasashe goma sha daya da suka sami nasarar yaki da zazzabin cizon sauro da kashi 50% ; yayinda a kalla gidaje 45% suke amfani da gidan sauron da aka yiwa feshi da magani; kashi 35% na kananan yara kuma suke kwana a karkashin gidan sauron da aka yiwa feshi da magani.

Dr. Sambo ya bayyana cewa kalubalan da kasashen nahiyar Afrika ke fuskanta a yaki da zazzabin cizon sauro sun hada da rashin ingantattun hanyoyin sa ido, da matakan kula da aiwatar da shirin, da rashin hanyoyin binciken kwakwa da kuma rashin aiwatar da tsare tsaren da aka shinfida na yaki da cutar kamar haramta sayarwa ko amfani da magungunan zazzabin cizon sauro da ake sha ko kuma amfani da su wajen kashe sauro, wadanda bincike ya nuna basu da amfani.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG