Accessibility links

Kwararru sun jadada muhimmancin shayar da jarirai da nonon uwa


Wata mace tana ba jaririnta dake fama da tomowa ruwa.

An yi kira ga iyaye su kara maida hankali wajen bada fifiko kan shayar da jarirai da nonon uwa, sabili da sinadarai da ke akwai da jariri yake bukata , hadi da ruwa da zai taimaka mashi ya gima cikin koshin lafiya a watannin shida na farko da haihuwa

An yi kira ga iyaye su kara maida hankali wajen bada fifiko kan shayar da jarirai da nonon uwa, sabili da sinadarai da ke akwai da jariri yake bukata , hadi da ruwa da zai taimaka mashi ya gima cikin koshin lafiya a watannin shida na farko da haihuwa.

Ministan lafiya na Najeriya Farfesa Onyebuchi Chukwu ne ya yi wannan kiran yayin kaddamar da makon shayar da jarirai da nonon uwa da aka yi a birnin tarayya Abuja.

Farfesa Chukwu ya bayyana cewa, duk da kokarin da gwamnati ke yi na ganin ana ba jarirai nono zalla a watanni shida na farko da haihuwarsu, ba a shayar da jarirai da dama da nono zalla. Dalili ke nan da taken makon shayar da jarirai da nonon uwa na shekarar da ta gabata ya maida hankali kan cike gibin dake akwai a yunkurin cimma wannan burin.

Bisa ga cewar ministan, ci gaba da aka samu a fannin sadarwa dama ce ta samar da bayanai kan shayar da jarirai da nonon uwa zalla ga duk mai bukata a lokaci da kuma inda akwai bukata. Sabili da haka ya nemi hadin kan dukan wadanda wannan hakin ya rayawa a wuyansu da kuma kafofin sadarwa da kwararru a fannin kiwon lafiya, su hada hannu da gwamnati wajen inganta lafiyar kananan yara a Najeriya.

A halin da ake ciki kuma asusun tallafawa kananan yara na duniya UNICEF ya yi kira ga abokan hadin guiwar asusun a duk fadin duniya su kara kaimi wajen wayar da kan al’umma kan muhimmancin shayar da jarirai da nonon uwa.

A cikin sanarwar da ya bayar, darektan asusun Anthony Lake, yace yanzu lokaci ya yi da za a kai wannan kamfen ba a dakunan haihuwa da asibitai kadai ba, amma ga alu’mma baki daya a kasashe masu tasowa da kuma kasashe masu arziki domin su fahimci muhimmancin shayar da jarirai da nonon uwa tun kafin su zama iyaye.

Darektan UNICEF ya bayyana cewa, ana bukatar daukar kwararan matakan isar da wannan sako mai muhimmanci cewa “Shayar da jariri da nono zai iya ceton ranshi. Babu wani rigakafin da yafi shi arha da sauki wajen rage yawan jarirai da suke mutuwa kafin su cika shekaru biyar da haihuwa”

XS
SM
MD
LG