Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sami Koma Bayan 'Yancin Walwala A Duniya - Frededom House


Freedom House, logo
Freedom House, logo

Wata kungiyar kare hakkin Bil'Adama dake nan Amurka da ake kira Freedoom House da turanci ta fidda wani sabon rahoto dake cewa an sami koma bayan 'yancin walwala a fadin duniya a shekarar da wadda ta wuce shakaru 11 a jere. Koma bayan, kungiyar ta aza laifin sanadiyar karuwar kishin kasa a kasashe da suke bin tafarkin demokuradiya.

A safiyon da tayi,kungiyar ta auna kasashe 195, a cikinsu kashi 45 cikin dari an ce suna da 'yanci. Kashi 30 cikin dari suna da kwariya kwariyar 'yanci, kana kashi 25 an ce basu da 'yanci.

Rahoton yace kasashe 67 da suke bin tafarkin Demokuradiyya sun sami koma bayan 'yancin siyasa dana walwala a bara, da suka hada da kasashe kamar su Brazil, da Faransa, da Jamus da kuma Amurka. Rahoton yace kasshe 36 ne kadai suka sami ci gaba ta fuskar 'yanci.

Mai magana da yawun kungiyar Sarah Rapucci wacce ta yi magana da Murya Amurka daga New York tace kasar da ta fi ko wacce samun koma baya a bara itace Turkiyya. A nan ne aka fara ganin hana walwalar 'yan jarida kamin ma juyin mulkin da aka yi da bai sami nasara ba.

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG